rss

Amurka ta Sanar da Ƙarin Tallafin Taimaka wa Waɗanda Bala’i ya Shafa ga Ƙasashen Afrika Masu Fuskantar Matsanancin Ƙarancin Abinci

English English, Français Français, Português Português

Sashen Harkokin Wajen Amurka
Ofishin Kakaki
Domin yaɗawa nan da nan
Tanbihin kafofin yaɗa labarai
6 ga watan maris 2018

 
 

A yau, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson ya bayyana kusan dala miliyan 533 na ƙarin tallafi ga mutanen Habasha, Somaliya, Sudan ta Kudu, da Najeriya, kuma da ƙasashen yankin Tabkin Chadi, inda miloyoyin mutane suke fuskantar ƙarancin abinci da ke barazana ga rayuka da kuma rashin abinci mai gina jiki sakamakon ci gaban rikici ko fari na dogon lokaci.  Duk da yake ba da tallafi ga waɗanda suke fuskantar bala’i ya kasance muhimmin abin ceton rai ne, wannan tallafi ba zai magance waɗannan masifofi ba, waɗanda mafi yawancinsu mutun ne kan haddasa su.

Da wannan sabon tallafin daga Ma’aikatar Harkokin Waje da kuma Hukumar Raya Kasashe Masu Tasowa ta Amurka USAID, Amurka tana samar da agajin abinci na gaggawa da mai gina jiki domin taimakon al’ummomi marasa ƙarfi, ciki har da dubban tan na ainihin agajin abinci. Kuma kuɗin yana ɗaukar nauyin tsare-tsare na samar da ingantaccen ruwan sha, kiwon lafiya na gaggawa da kuma na tsabta domin magance da kuma hana yaɗuwar cuta, tare da sake haɗa iyalai waɗanda suka rabu sun rabu dalilin tashin hankalin rikici. Wannan tallafin ya kuma haɗa da muhimman kayan aikin likita, kayan tsabta na armashi da kuma wurin kwanciya, tare da ba da fifiko ga tsare-tsaren da suke kare rukunan marasa ƙarfi.

Daga cikin sabbin kuɗaɗen da aka bayyana, kusan dala miliyan 184 ne aka keɓe wa al’ummomin Sudan ta Kudu waɗanda bala’i ya shafa, fiye da dala miliyan 110 domin al’ummomin Habasha da waɗanda bala’I ya shafa, fiye da dala miliyan 110 domin al’ummomin da bala’i ya shafa a Somaliya, kuma fiye da dala miliyan 128 don al’ummomi waɗanda bala’I ya shafa a Najeriya da kuma ƙasashen yankin Tabkin Chadi.

A yankin Tabkin Chadi da Sudan ta kudu, shekaru da dama na riciki sun haddasa matsanancin ƙarancin abinci. A Somaliya, tashin hankalin da ke ci gaba ya daɗa wahalar da mutane ke ji daga matsananci fari na tsawon lokaci. A Habasha, fari mai ci gaba ya ƙara tsananin yanayin wadatar abinci wadda a da ma a taɓarɓare take.  Saurin kwararowar taimako daga Amurka, tare da na wasu masu ba da tallafi dabam, yana taimakawa wajen inganta yanayin rayuwar mutane a cikin dukkan waɗannan ƙasashen.  Amma a ƙarshe dai shugabanin waɗannan ƙasashen, har dai ma na Sudan ta Kudu, su ne za su tsada shawarar tsayar da tashin hankalin su kuma mayar da jin daɗin rayuwar jama’arsu makasudin farko a ayukansu. Miliyoyi za su ci gaba da kasancewa cikin haɗari matsawar waɗanda suke jigajigan waɗannan rikice-rikicen suna ci gaba da faɗa. Amurka tana kira ga duk ɓangarin da ke cikin waɗannan rikice-rikicen da su ba masu aikin agaji damar isa wurin al’ummar da ke bukatar taimako cikin kwanciyar hankali kuma ba tare da an yi musu katsalandan ba.

Amurka ce mai tallafawa al’umma da bala’i ya shafa mafi girma don waɗannan matsaloli a Afrika, ta ba da kusan dala biliyan 3 tun farkon kasafin kuɗin shekara na 2018. Muna yabawa da gudumawa wajen agaji ga al’ummomi da duk masu ba da tallafi suka yi, da kuma goyon baya ƙarin gudunmawa don cimma biyan bukatun da ke ci gaba da ƙaruwa.


Sakonnin Email
Domin samun sakonnin mu ko kuma ganin zabin da ka yi a matsayin mabiyin mu, shigar da bayanan ka a kasa