rss

BATU: DANGANTAKA TSAKANIN AMURKA DA AFRIKA: SABON TSARI

English English, Русский Русский

Sakataren Harkokin Wajen Amirka Rex Tillerson
Batu: Dangantaka Tsakanin Amurka Da Afrika: Sabon Tsari
Maris 2018

 
 

[Gabatarwa]

Na gode Dakta Cabrera – A ko da yaushe ina alfaharin haduwa da tsohon dalibin Fullbright, musamman ma idan inginiya ne kamar ni. Mu na mika godiya ga Jami’ar George Mason da ta bamu guri domin yin wannan jawabi da sashen karatun Ilimin nahiyar Africa da ‘yan Afrika mazauna Amurka game da ayyukan da suke yi a wasu daga cikin bangarorin da za mu tattauna a yau.

A wannan makon, zan kai ziyarar aiki a karon farko zuwa Nahiyar Afirka yankin Sahara – ziyarar da muka fara shiryawa tun watan Nuwamba a wani taron kasashen Afrika 37 da Tarayyar kungiyar kasashen Afrika. Abubuwan da muka tattauna a lokacin sun hada da yaki da ta’addanci, demokradiyya da tsarin mulki, bunkasa kasuwanci da zuba hannun jari a nahiyar – Zan kara bayani game da wadannan batutuwa nan ba da jimawa ba.

A rayuwata ta baya, na shafe tsahon lokaci a Nahiyar Afrika. Na yi imanin cewa akwai hanyoyi da dama a Nahiyar – na bunkasar tattalin arziki, samun ci gaba, da kuma fuskantar matsalolin da duniya ke fama da su ta hanyar kulla alaka mai cike da mutunta juna. Zan ji dadin komawa na share fagen kulla alaka mai karfi tsakanin kasar Amurka da Nahiyar Afrika. Wannan kuma ya kunshi ziyartar kasar Chadi, wacce a tarihinta,  ba ta taba bakuntar sakataren harkokin wajen Amurka ba.

[Tsarin alaka tsakanin Amurka da Afirka + Dabarun Muhalli]

A karnin da ya gabata, a yayin da Nahiyar Afrika ke fita daga zamanin mulkin mallaka, an samu karin dankon dangantaka tsakanin Amurka da Nahiyar. Ma’aikatar harkokin waje ta kafa hukumar kula da ayyukan kasashen Afrika a shekarar 1958 – shekara guda bayan mataimakin shugaban kasa a lokacin, Richard Nixon ya ziyarci Nahiyar.  Kasar Ghana ta gayyaci mataimakin shugaban tare da Martin Luther King Jr domin su halarci shagulgulan zagayowar ranar samun ‘yancin su. Wannan lamari ya faru daidai shekaru 61 da suka gabata.

Shekaru kadan bayan haka, shugaban kasa John F. Kennedy ya kafa hukumar USAID da nufin bunkasa Nahiyar Afrika, sannan ‘yan aikin agajin mu na farko a karkashin kungiyar fafutikar zaman lafiya suka isa kasar Ghana da Tanzaniya. Shekaru 40 da suka gabata a wannan wata, shugaban kasa Jimmy carter ya ziyarci kasashen Laberiya da Nijeriya inda ya sanar da cewa “kasar mu ta kaikatar da hankalinta ga Nahiyar Afrika, lamarin da bai taba faruwa ba a baya.

A yau, wannan kaikatarwar za ta ci gaba. Zaman lafiyar mu da ci gaban kasar mu na da alaka mai karfi da na nahiyar Afrika, fiye da yadda ake gani a baya. Wannan kuma zai kara karfafa ne a shekaru masu zuwa a sakamakon wadannan dalilai:

Na daya: Sauyi a adadin jama’a. Nan da shekarar 2030, kimanin kaso daya bisa hudu na ma’aikatan duniya za su fito ne daga Nahiyar Afrika. Zuwa 2050, an kiyasce cewa adadin mutanen Nahiyar zai ninka zuwa kusan biliyan 2.5, inda kimanin kaso 70 cikin dari ba za su wuce shekaru 30 ba.

Na biyu: Afrika na fuskantar ci gaba mai karfi a bangaren tattalin arziki. Bankin Duniya ya kiyasce cewa shida a cikin kasashe goman farko na duniya da za su fi bunkasar tattalin arziki a wannan shekarar, kasashen Afrika ne.

Idan aka danganta, zuwa shekarar 2050, Nijeriya za ta zama mai adadin jama’a sama da kasar Amurka da tattalin arziki da ya haura na kasar Australia.

Domin a fuskanci inda duniya ta nufa, dole a fuskanci cewa Afrika ita ce makoma.  Afrika za ta taka rawa mai karfi a kalubalen da duniya ke fuskanta a bangarorin tsaro da tattalin arziki. Haka zalika a bangaren damarmakin fadadawa a fannin bunkasar tattali arziki da samun tasiri.

Yayin da nahiyar ke cike da banbance banbance na mutane, al’adu da gwamnatoci, akwai abubuwan da ta kunsa na damarmaki da kalubale masu kamancecenuwa da juna. Muhimmancin Nahiyar ya fito fili ne idan aka yi la’akari da matasan ta, amma yawan adadin matasa na nufin a na bukatar karin ayyukan yi. A yayin da aka samu dadi a adadin mutanen Afrika da ke fita daga talauci, kasashen za su bukaci ci gaba da bunkasa a samar da ababan more rayuwa. Wadannan matasa da ke kara yawa idan aka bar su babu ayyukan yi da burin samun rayuwa mai inganci za su kirkiro da sabbin hanyoyin ta’addanci domin cutar da ‘yan baya masu zuwa, hana samun zaman lafiya da gwamnatocin demokradiyya. Zai kasance dole sai shugabanni sun yi tunani mai zurfi domin kirkiro sabbin hanyoyin tsantseni da ‘yar dukiyar da suka malaka.

A yayin da muke duba ga nan gaba, wannan gwamnati na neman karfafa dangantakar ta da Nahiyar Afrika, da nufin taimaka mata wajen tsayawa da kafafunta da kara jimirinta.  Wannan zai yi wa abokan huldar mu dadi kuma muma ya mana dadi domin kuwa zai tabbatar ‘ya’yan mu da jikokin mu sun samu makoma mai cike da kwanciyar hankali.

[Tsaro]

Makomar zaman lafiya ta ta’allaka ne akan tsaro – wanda shine tushen samar da ci gaban tattalin arziki da hukumomi masu karfi. Idan babu tsaro, babu bangaren da ya ke kasancewa daidai.

A yau, yawaitar ayyukan ta’addanci na barazana ga makomar mutane da dama. A watan Agusta mai zuwa, za mu tuna daruruwan rayukan da muka rasa shekaru 20 da suka gabata a ofishin jakadancin Amurka a Nairobi da Dar es Salam.

Bayan wannan ranar, ‘yan ta’adda sun ci gaba da kashe dubunnan mutane a nahiyar Afrika. Hare-haren ta’adanci ya karu daga kasa da 300 a shekarar 2009 zuwa kimanin 1500 a kowacce shekarar 2015, 2016 da 2017. A kwana kwanan nan, mun kara wayar ido da sace ‘yan mata sama da 100 a Nijeriya, an raba su da iyayen su, an kuma sauya makomar rayuwar su har abada.

A makon da ya gabata, a matsayin martani ga ci gaban barazanar da ake fuskanta, Na zaba kuma gwamnatin Amurka ta sanya takunkumi ga kungiyoyi bakwai da ke da alaka da kungiyar ISIS, a ciki har da ISIS ta Nahiyar Afrika ta yamma da ISIS ta kasar Somaliya da shugabannin su a wani yunkuri na dakile hanyoyin samun kudin da suke amfani da su wajen kaddamar da hare-hare.

Domin samun nasara akan wannan annoba, kasar Amurka ta mayar da hankali wajen aiki da abokan huldar ta a nahiyar Afrika da nufin kakkabe matsalar ta’addanci daga Nahiyar da ma duniya baki daya, ta hanyar magance abubuwan da ke haifar da tarzoma, wanda shine sillar tsaurara ra’ayoyin mutane da shigar da su kungiyoyin ta’addanci tun da fari, da kuma bunkasa hukumomin tsaron kasashen Afrika. Mu na so mu taimaka wa kasashen Nahiyar wajen samar da tsaro ga mutanen ta ba tare da keta doka ba.

A yau kasashen Afrika na yunkurowa wajen yin abunda ya kamata, tare da fuskantar kalubalen da ke zuwa da irin wannan mataki

Ta’addanci bai san da iyaka ba. A yankin dajin Sahel da tafkin Chadi, Boko Haram, ISIS, sashen Nahiyar Afrika ta yamma, Al Qaeda a wasu yankunan, sun samu gurin zama sun saba kuma suna iya kai hare-hare a duk lokacin da suka so. Hadin kai tsakanin yankuna na da muhimmacin wajen dakile wadannan hare-hare da hana aukuwar su a nan gaba.

Rundunar hadin gwiwar kasashe ta MNJTF – wacce kasashen Nijeriya, Chadi, Nijar, Benin, da Kamaru – tare da gamayyar kasashen yankin Sahel ko G5 – wato Burkina Faso, Chadi, Mali, Moritaniya da Nijar – na hada dukiyoyin su guri guda da iyawar su. Wannan aikin da suke yi na da muhimmanci wajen kawo karshen tashin hankula da ta’addanci a daga cikin gida.

A watan Oktobar bara, na sanar a cewa kasar Amurka za ta kara nauyin gudunmawar da ta ke baiwa wannan yunkuri na kai da kai. Mun bada kyautar kudaden da suka kai dala miliyan 60 ga yunkurin yaki da ta’addanci a kasashen kungiyar G5 domin taimaka masu wajen horaswa da samar da kayan aiki ga rundunar hadakar da suka hada, da wayar da kan jama’a game da illolin ta’addanci a cikin al’umma.

Bugu da kari, a cikin sama da shekaru 10 da suka wuce, kasar Amurka ta tallafawa yunkurin hadin gwiwa da kasashen Afrika na yankin Sahara ke yi na yaki da ta’adanci tare domin samar da horaswa da bunkasa hadin kai tsakanin rundunar sojoji, jami’an tsaro da fararen hula a fadin Arewa da Yammacin Afrika. Irin wannan tsarin tallafi muka yi amfani da shi a Nahiyar Afrika ta Gabas, da shirinmu na hadin gwiwar kasashen yankin Afrika ta Gabas wato CT ko PREACT. Tun a shekarar 2016, kasar Amurka ta bada gudunmawar sama da dala miliyan 140 domin taimakawa abokan huldar ta wajen hana ‘yan ta’adda samu maboya da daukan sabbin mutane.

Kasar Amurka na godiya ga shugabancin gamayyar kungiyoyin Afrika, AU game da rawar da ta ke takawa mai girma kuma wacce ta shafi bangarori da dama. Aikin jakadancin Tarayyar kungiyar kasashen Afrika AU a Somaliya – AMISON – wanda ya kunshi aika dakaru daga kasashen Afrika biyar ya taikama wajen wanzar da zaman lafiya a yankunan da Al Shabaab ke kai hare-hare da kuma tabbatar da cewa mutanen kasar Somaliya sun samu irin taimakon da suke bukata. Zan ji dadin haduwa da shugabar kungiyar AU, Faki a ziyara ta gaba domin mu tattauna yadda za mu yi aiki tare wajen kawo karshen ta’addanci a yankin.

Rawar da kasar Amurka za ta taka a wannan fanni shi ne na horaswa domin tabbatar da dogaro da kai, ba wanda za a dogara akan ta ba – ta yadda abokan huldar mu za su iya samarwa kan su tsaro. Wannan ya yi daida da tsarin mu na fafutikar samar da zaman lafiya a Nahiyar.

A matsayin mu na kasar da ta fi samar da horaswa a fannin wanzar da zaman lafiya a Nahiyar Afirka, mu na aikawa tare da barin dakarun mu a kasashe domin su bada gudunmawar su a yaki da ta’addanci, cire boma-boman da aka binne, da kuma tabbatar da sauyin gwamnati ba tare da tarzoma ba. Wannan ya na samar da tsaron da ke bada damar kai abinci, kiwon lafiya da sauran ababen tallafi ga guraren da ake bukatar su.

A shekarar da ta gabata, kasar Amurka ta dauki nauyin maikatan wanzar da zaman lafiya a Afrika sama da guda 27,000 daga kasashe sama da 20 na Afrika. A nan ma, kasashen Afrika da dama sun dauki lamuran su a hannun su. A shekaru 10 da suka wuce, kimanin kaso 20 cikin dari na jami’an wanzar da zaman lafiya ne kadai ke fitowa daga kasashen Afrika. A yau, wannan adadi ya haura kaso 50 cikin dari.

A yayin da muke daukan nauyin ayyukan inganta tsaro, ya kuma zama wajibi mu nemi mafita mai daurewa a diflomansiyyance domin kawo karshen wahalar jama’a. Har izuwa lokacin da za mu cimma wannan, Amurka a matsayin ta na kasar da ta fi bada tallafi a duniya za ta kasance tare da kasashe masu rauni.

Domin tabbatar da jajircewar mu game da wannan kudiri, a yau ina sanar da tallafin kusan Dala miliyan 533, wanda kari ne akan tallafin da muka bayar na yaki da yunwa da sauran bukatu a kasashen Somaliya, Sudan ta Kudu, Habasha da Yankin Tafkin Chadi. Yunwa ta tazzara ne a wadannan yankuna saboda ayyukan wasu mutane. A yayin da ake samun tashin hankali, mutane kan bar gidajen su, a cikin wannan hali, ba za su iya noma ba kuma yawancin lokuta su kan rasa hanyoyin samun abinci, ilimi da kiwon lafiya. Da yawa kan rasa komai. Sannan wani lokacin akwai matsalar sauyin yanayi, kamar a wasu bangarorin Afrika inda rashin ruwan sama na tsahon lokaci ke haifar da matsanancin rashin abinci.

Wadannan karin kudaden tallafi za su taimaka wajen samar da abinci na kar-ta-kwana, samar da abinci mai amfani da ruwan sha mai tsafta, tan dubunnai na abinci da shirin samar da kiwon lafiya ga miliyoyin mutane domin dakile yaduwar cututtuka masu barazana ga rayuwa kamar amai da gudawa. Wannan zai ceto rayuka da dama.

Mutanen kasar Amurka kamar yadda aka saba, na hulda da kasashen Afrika wajen tabbatar da cewa mutanen su da ke bukatar taimako sun samu tallafin da zai ceci rayuwar su. Mu na kira ga sauran kasashe da su bi sahun mu wajen bayarda agajin da nahiyar ke matukar bukata. Mu na fata cewa wannan yunkuri namu zai karawa wasu karfin gwiwar bada na su tallafi domin mu raba nauyin da ke kanmu, mu kuma kawo karshen wahala a Afrika.

Sai dai wannan tallafi na mu ba zai kawo karshen tashin hankulan da ake samu ba, amma zai siya mana lokaci – lokacin da za mu iya gano mafita a diflomansiyyance.

[Taimako a fafutikar da mu ke na neman zaman laifya cikin lumana]

A yayin da kasashen Afrika da dama ke daukan matakin kawo karshen matsalolin su na cikin gida, kasar Amurka na bukatar su a matsayin abokan hulda da su samawa kansu guri a matakin duniya baki daya. Daya daga cikin bangarorin da muke bukatar hadin gwiwa shi ne fafutikar mu ta lumana na kawo kasar Koriya ta Arewa kan teburin sulhu

Kasar Koriya ta Arewa na barazana ga duniya baki daya da shirye shiryen ta na sarrafa makaman Nukiliya ba bisa kai’da ba da sauran ayyukan katsalandan, a ciki har da fitar da makaman sayarwa zuwa Nahiyar Afrika. Wannan ba kawai ya shafi abokan huldar mu bane a Nahiyar Turai da Asia. Ba kawai ya shafi kasashen da ke da alaka da Koriya ta Arewa ba, kamar  kasar Sin da Rasha. Wannan abu ne da ya shafi duniya baki daya.

A watan da ya gabata, a yayin da na kai ziyara ta farko Kudancin Amurka, na yi magana da takwarorina game da hanyoyin da suke bi wajen bada gudunmawar su ga wannan fafutikar wanzar da zaman lafiya.

Ya kamata kasashen Afrika su shiga wannan lamari.

Kasashen Angola da Senegal sun dauki wasu matakai na sanya takunkumi ga kasar da zai shafi tattalin arzikin ta. Gwamnatin kasar Habasha ta sanar da aniyar ta na bayar da taimako. Amma kasashen Afrika da dama na nokewa. Mu na fata za su kara muryoyin su akan na sauran al’ummar duniya domin kawo karshen wannan matsala ta diflomasiyya, tattalin arziki da sarrafa makamai a kasar Koriya ta Arewa.

[Kasuwanci, Hannun jari, da bunkasar tattalin arziki]

Samun tsaro a nahiyar Afrika abu ne da zai haifar da ci gaba mai girma. Samun kwanciyar hankali zai ja hankalin masu zuba hannun jari a Afrika daga kasar Amurka , wanda hakan zai kawo ci gaban bunkasar tattalin arziki, ya kuma yi doriya akan nasarar da muka cimma da dokar baiwa Afrika damarmakin kara bunkasa; AGOA.

Dokar AGOA ta kasance jigon manufofin kasuwancin Amurka a kasashen Afrika na tsahon kusan shekaru ashirin. Ta hanyar AGOA, mun ga ci gaba da dama. Kasuwanci da ba shi da alaka da man fetur ya ninka sama da gida biyu – daga dala biliyan 13 a shekara zuwa kusan dala biliyan 30 a shekara. A bara, kasuwancin Amurka ya kai dala biloyan 38.5 – wanda kari aka samu akan dala biliyan 33 a shekarar 2016.

Muna samun karin karfin gwiwa duba da wasu matakai da abokan huldar mu na Afrika ke dauka a yunkurin kara fadada cinikayya tsakanin mu da su. A ziyarar da ya kawo kasar Amurka a makon da ya gabata, Shugaban kasar Ghana, Akufo-Addo ya yi jawabi ga kungiyar gwamnoni ta kasa – ya kasance shugaban wata kasa a Afrika na farko da ya yi haka. Ya yi magana game da burin shi – burin mutanen shi na fita daga talauci zuwa wadata a ‘yan shekaru masu zuwa. Kasar Amurka na son tallafawa gwamnatoci da ‘yan kasuwa masu zaman kan su a kasashen Afrika da ma a nan gida domin tabbatar da an cimma haka.

Afrika na kunshe da dumbin ma’adanai kasa da ba a taba ba. Kwarewar ‘yan kasuwar kasar Amurka zai iya taimakawa wajen hako wadannan ma’adanai, wanda zai taimaka wajen fitar da mutanen Afrika da dama daga cikin talauci idan suka ci moriyar wadatar arziki da wadannan ma’adanai za su kawo.

Amma domin a bunkasa tattalin arziki, a kawo ci gaba a kuma karfafa kasuwancin kasa da kasa a Nahiyar, ana bukatar ababen more rayuwa na Nahiya da Nahiya.

A yau, kimanin kaso 12 bisa dari kacal na kayayyakin da ake sarrafawa a kasashen Afrika ake fitarwa kasashe masu makobtaka a Nahiyar domin sayarwa. Idan aka kwatanta wannan da kaso 25 bisa dari na Nahiyar Asia da sama da kaso 60 na Nahiyar Turai, za a ga cewa akwai damar samun ci gaba ta fannin kasuwanci a Nahiyar.

A yayin da kasashen Afrika ke ci gaba da tsuke iyakar da ke tsakanin su ta hanyar rage harajin shigar da kayyaki, bunkasa fannin sifiri, makamashi, ababen more rayuwa, za a samar da karin damarmaki ga ‘yan kasuwar kasar Amurka a fannin zuba hannun jari da kasuwancin a tsallaken tekun Atlantic.

Kwarewar dan kasuwar Amurka da ke shigo da kayayyaki da kasashen waje da ayyukan shi su ne gamin da zai taimakawa makomar Afrika: ta hanyar bada tallafi a fannin tattalin arziki, koyawa kasashen Afrika sabbin dabaru, da yin hakan da bayyanannen tsari. Wannan shi ya sa muke son kafa sabuwar hukumar bunkasa tattalin arziki; FDI. FDI bankunan gwamnati ne na musamman da ake kafa su domin tallafawa ‘yan kasuwa masu zaman kansu domin su samu ci gaba. Muna aiki tare da majalisar kasar nan wajen ganin an baiwa kasar Amurka damar karawa a kasuwance da kasashe masu tasowa da suka cimma nasara ta wannan fanni.

Shirin Power Africa, wanda ke karkashin hukumar USAID ya na daya daga cikin mafi girman hadin gwiwa tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa masu zaman kansu a tarihin Nahiyar. Power Africa wanda aka kafa shi shekaru 5 da suka gabata na da nufin tallafawa kasashen Afrika wajen samun abu mafi muhimmanci da zai kawo ci gaba, wato wutar lantarki. A yau miliyoyin mutanen Afrika – a fadin yankin sahara – sun samu wutar lantarki saboda yunkurin da kamfanoni masu zaman kan su sama da 140 suka yi wajen tabbatar da haka. Burin mu shi ne mu samar da megawat na wutar lantarki dubu 30 nan da shekarar 2030 – ko kuma joni guda miliyan 60 da zai samar da wutar lantarki ga mutane miliyan 300 a Nahiyar Afrika.

A makon da ya gabata kawai, Jami’in gudanarwa Green ya sanar da rukuni 2 na shirin domin fadada damarmakin da shirin ke samarwa.

Kasar Amurka ta kagu ta kawar da abubuwan da ke haifar da cikas a fannin kasuwanci da zuba hannun jari da abokan huldar mu, wanda zai taimakawa kasashen Afrika su fita daga dogaro da wasu su shiga dogaro da kan su; su kara adadin masu kudin da suke da shi da kara tattalin arzikin su cikin na duniya gaba daya.

[Ilimi + kiwon lafiya]

Domin mu yi shirin zuwan nan gaba tare da kai Nahiyar Afrika matsayin da ya kamata, ana bukatar ma’aikata masu ilimi da lafiya. Wannan haka ya ke a ko’ina a duniya, amma duba da adadin matasan da ke Nahiyar Afrika, za a iya cewa wannan abu ya fi muhimmanci a can.

Shirin koyar da matasa dabarun shugabanci mai suna YALI na daya daga cikin hanyoyin da ma’aikatar harkokin wajen Amurka da hukumar USAID ke kashe kudade wajen samar da hazikan matasa a nahiyar Afrika. YALI na samar da horaswa ta shugabanci da na aiki ga hazikan matasa a Afrika a bangarori kamar samar da ‘yanci ga kafafen yada labarai, samar da hukumomi masu jurewa har ma da yadda ake fara sana’o’i. A yau, YALI na da mambobi sama da dubu 500 daga kowacce kasa a Nahiyar Afrika, yankin sahara.

Ta bangaren shirin shugaban kasa na kai agajin gaggawa ta fannin cutar kanjamau, wanda ake kira PEPFAR, kasar Amurka ta sauya yanayin tallafin da duniya ke bayarwa game da cutar kanjamau. Babu inda za a ga tasirin wannan abu kamar a Afrika.

A lokacin da aka kaddamar da shirin PEPFAR shekaru 15 da suka gabata samun cutar a jikin nutum kamar yanke masa hukuncin kisa ne kuma a haka iyalai da al’ummomi da dama suka yi ta kamuwa da cutar. Duniya ta fuskanci koma baya a fannin kiwon lafiya. A yankunan da abun ya fi kamari a kasashen nahiyar Afrika da ke yankin Sahara, yawan mace-macen jarirai ya ninku sau biyu, na kananan yara ya ninku sau uku, kuma matsakaicin shekarun da mutane ke shafewa a duniya ya ragu da 20. Mutum daya cikin kowanne uku na dauke da cutar kanjamau kuma an rasu an bar miliyoyin marayu kuma  mutane kimanin dubu 50 kadai ke samun magungunan ceton rai. A yau, shirin PEPFAR na samar da wadannan magunguna ga sama da mutane miliyan 13 da dubu dari 3 a fadin duniya. Saboda shirin, mata masu dauke da cutar kanjamau sun haifi jarirai miliyan 2 da dubu dari 2 wadanda ba sa dauke da cutar. Haka zalika mun samar da tallafi ga marayu, yara marasa galihu da masu kula da su sama da miliyan 6 da dubu dari 4.

Wannan gwamnati ta zage damtse wajen ganin an ceto rayuwar ‘yan Afrika. A watan Satumbar bara, na sanar da shirin PEPFAR na karfafa taimakon da ake yi a fannin cutar kanjamau daga shekarar 2017 zuwa 2020. Wannan shiri zai shinfida fagen magance cutar a kasashe sama da 50 a cikin shekaru uku. Ya zayyana hanyoyin da za mu bi wajen kara karfafa ayyukan da muke yi a kasashe 12 da cutar kanjamau ta fi kamari a Afrika, wadanda kuma aka kiyasce za su kakkabe cutar nan da shekarar 2020. Hakika mun hango kakkabe kanjamau daga fadin duniya nan ba da dadewa ba. Lokacin ya kusa zuwa, kuma wannan na da nuhimmanci ga makomar Afrika.

[Samar da gwamnatocin demokradiyya]

Domin tabbatar da an samu dorewar tsaro, kasuwanci da zuba hannun jari, ci gaban tattalin arziki, dole sai an samu gwamnatoci masu aiki da gaskiya, wadanda jama’a suka yarda da su. Zaman lafiya da ci gaba zai iya yiwuwa ne kawai a al’ummar da ta rungumi demokradiyya. ‘Yancin kafafen yada labarai, ‘yancin fadin albarkacin baki, ‘yancin addini, da kungiyoyin jama’a na taimaka wajen kirkiro hanyoyi na ci gaban tattalin arziki. A yau Afrika za ta ci moriya idan ta karfafa demomradiyyar ta, ta yadda ra’ayoyin ‘yan kasa za su samu matsayi na muhimmanci, tare watsi da cin hanci da rashawa da bunkasawa tare da kare hakkin ‘yan adam.

Tarayyar kasashen Afrika AU ta kiyasce yadda Afrika ta rasa biliyoyin daloli a sakamakon cin hanci da rashawa – biliyoyin dalolin da aka kasa zubawa a fannin ilimi, ababan more rayuwa da tsaro.

Cin hanci da rashawa na barin jama’a cikin talauci, ya kara tazarar dukiya tsakanin masu kudi da marasa shi da kuma rage amincewar da mutane ke yi wa gwamnati. Zuba hannun jari kan raguwa yayin da rashin tsaro da tashin hankali ya ke kara ta’azzara, lamarin da ke haddasa tsirowar ta’addanci da tarzoma. Muna goyon bayan AU da ta zabi batun cin hanci da rashawa a matsayin batun tattauna a taron ta na wannan shekara. Mu na fata hakan zai share fagen mayarda hankali da kungiyar za ta yi akan cin hanci da rashawa a dawwame kuma na tsahon lokaci.

Domin nuna goyon bayan ta ga wannan batu, Amurka za ta ci gaba da aiki tare da kasashen Afrika domin karfafa demokradiyyar su. A watan da ya gushe, ma’aikatar harkokin waje ta bukaci Majalisa ta amince da dala miliyan 137 domin taimakawa kasashen da suka bada muhimmanci ga bunkasa demokradiyya, ‘yancin ‘yan adam, tsarin mulki na gaskiya, rage cin hanci da rashawa da hadin gwiwa sama da rikici da tashin hankali.

Demokradiyya na bukatar sauyin gwamnatoci ta hanyar gudanar da zabubbuka da gaskiya. Haka zalika ya na bukatar kungiyoyinjama’a, da bangaren yada labarai masu ‘yancin da za su wayar da kan jama’a su kuma kusantar da su ga gwamnatocin su. A bara, kasar Amurka ta taimaka a zaben Laberiya wanda aka yi cikin zaman lafiya da lumana – wannan kasa ta jima ba ta samu sauyin gwamnati da bai zo da rikici ba. Abubuwan da muka yi sun hada da wayar da kan masu zabe tare da mayar da hankali a kan matasa, mata da masu zabe a karon farko, tare da kuma da aiki da kafofin yada labarai wajen ganin sun bada rahotannina gaskiya.

Kudaden tallafin na tabbatar da gaskiya a yadda gwamnatoci  ke kashe kudade, wato FTIF ya taimaka wajen ganin gwamnatoci sun inganta kasafin kudaden su tare da bayyana su a fili ga jama’ar su, wanda hakan ya baiwa kungiyoyi damar bada shawarwarin gyara. A yanzu haka kasar Amurka na da ayyuka 31 a wannan fanni –  kuma ta na shirin fitar da kudi ga dadin guda 9 a fadin Nahiyar Afrika. Tuni wadannan kudade suka tallafawa kasashen Chadi, Kenya da Malawi wajen yaki da cin hanci da rashawa da yi wa jama’ar su aiki.

Haka kuma idan ana maganar samun ci gaba, muna sanya shirye-shiryen samar da gwamnatoci na gari a ciki. A matsayi na na sakataren harkokin waje, ni ne shugaban hukumar MCC. Ta wannan hukuma wacce aka kafa domin rage talauci, kasar Amurka na bada lada ga gwamnatoci na gari – masu gaskiya – ta hanyar hada su da kudaden tallafin samun ci gaba. Kimanin kaso 60 na wadannan kudade na zuwa Nahiyar Afrika ne. A watan Nuwambar bara, mun baiwa kasar Cote d’Ivoire tallafin dala miliyan 524 domin ta bunkasa ilimi da harkar sifirinta. Wannan ya yiwu ne kadai bayan kasar ta fitar da manufofin bunkasa ‘yancin kasuwanci, manufofin demokradiyya, hakkin ‘yan adam da yaki da rashawa – wanda ya haifar wa kasar garambawul kafin a kashe dala daya ta kudaden harajin mutanen Amurka.

Wannan shi ne tsarin Amurka na samar da ci gaba kuma ya dade ya na aiki.

Kasar Amurka ta fi mayarda hankali ne akan ci gaba mai dorewa da ke karfafa hukumomi, doka da oda inda babu wankakke da mai, tare da taimakawa kasashen su tsaya da kafafun su. Mu na hada gwiwa da kasashen Afrika wajen basu ladan gudanar da mulki da gaskiya domin samar da tsaro da ci gaba mai dorewa.

Wannan tsari ya sha banban da na kasar Sin, wanda ke karfafa dogaro akan su – ta hanyar amfani da yarjejeniyar da ba a iya fahimta, bada bashi mai wuyar biya, da kasuwanci mai cike da rashin adalci wanda kuma ya ke sanya kasashe a cikin bashi ya kuma rage masu ‘yancin kan su, lamarin da ke hana su ci gaba mai dorewa. Babu shakka hannun jari daga kasar Sin zai iya taimakawa kasashen Afrika wajen samar da ababan more rayuwa, amma tsarin da suke bi ya haifar da karuwar basussuka da ayyukan yin da ba su taka kara sun karya ba a kasashe da dama. Idan aka hada da matsalolin siyasa da na samun kudaden shiga, wannan na barazana ga ma’adanan da ke kasashen Afrika da samun ci gaban arziki da kwanciyar hankali a dawwame.

Mu na maraba da wasu kasashen da za su taka rawa a ci gaban Nahiyar Afrika. Wannan shi ake nufi da ‘yancin kasuwanci – gasar da za ta samar da karin damarmaki. Amma muna son muga ci gaba mai amfani da gaskiya a harkokin kasuwanci da zai kawo ci gaba mai dorewa a cikin nahiyar. Muna fatan kasar Sin za ta biyo bayan mu a wannan yunkuri.

[Rufewa]

Kasar Amurka ta hango kyakkyawar makoma ga Nahiyar Afrika. Muna da damar kasancewa mun taka rawa a tafiyar nahiyar da zai kai ta ga ci gaba mai daurewa, kuma cike da kwanciyar hankali ga mutanen ta. Duka wadannan bangarori masu muhimmanci – kasuwanci da zuba hannun jari, mulki na gari, mutunta hakkin dan adam, magance ta’addanci da samun kwanciyar hankali – na da manufa iri daya: Taimaka wa kasashen Afrika su kai matsayin da za su iya kulawa da mutanen su.

Babu mafita mai sauki ga wadannan kalubale. Amma kasar Amurka a shirye ta ke ta magance su tare da hadin gwiwar kasashen Afrika, ta yadda nahiyar za ta zama guri na ‘yanci da ci gaba a karni na 21. Na gode da kuka bani lokacin ku.


Sakonnin Email
Domin samun sakonnin mu ko kuma ganin zabin da ka yi a matsayin mabiyin mu, shigar da bayanan ka a kasa