rss

Sanawar Ba da Kuɗaɗen Tallafi a Afrika

English English

USAID da kuma PRM Press Guidance
Maris 6, 2018
Manyan Bayani

 
 

 • Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya bayyana kusan dala miliyan 533 na ƙarin tallafi ga mutanen Habasha, Somaliya, Sudan ta Kudu, da Nijeriya, kuma da ƙasashen yankin Tabkin Chadi, inda miloyoyin mutane suke fuskantar ƙarancin abinci da ke barazana ga rayuka da kuma rashin abinci mai gina jiki sakamakon ci gaban rikici ko fari na tsawon lokaci.
 • Da wannan sabon tallafin, Amurka tana samar da agajin abinci na gaggawa da abinci mai gina jiki da sun haɗa da dubban tan na ainihin agajin abinci.
 • Amurka tana kuma ɗaukar nauyin tsare-tsare na samar da ingantaccen ruwan sha, da kuma kiwon lafiya na gaggawa da na tsabta domin magance da kuma hana yaɗuwar cuta, kuma da sake haɗa iyali waɗanda sun rabu dalilin tashin hankalin rikici. Tallafin na Amurka ya kuma haɗa da muhimman kayan aikin likita, kayan tsabta na armashi, da kuma wurin kwanciya, tare da ba da fifiko ga tsare-tsaren da suke kare rukunan marasa ƙarfi.
 • Amurka ita kaɗai ta kasance mai ba da tallafi ga al’umma da bala’i ya shafa mafi girma don waɗannan matsaloli. Muna ƙarfafa saura da su ƙara kashin kuɗaɗen tallafinsu don cimma biyan bukatar waɗannan bukatu na gaggawa, da ke ci gaba da ƙaruwa a Afrika.
 • Duk da yake wannan ba da tallafi ga waɗanda suke fuskantar bala’i ya kasance muhimmin abin ceton rai ne, nauyin biyan bukatun al’ummominsu da kuma kawo ƙarshen tashin hankali da rashin tsaron da ke haddasa waɗannan matsalolin, har dai ma a Sudan ta Kudu, a ƙarshe ya rataya ne a wuyan ɓangarorin da ke cikin waɗannan rikice-rikicen. Amurka tana kira ga duk shuwagabannin waɗannan ƙasashen da su sa fifiko ga jin daɗin al’ummominsu, su hana tashin hankali da kuma su daina yin katsaladan ga isar da kayan agaji zuwa ga mutane.

Idan an tambaya

Tambaya: Nawa ne Amurka ta bayar ga waɗannan ƙasashen?

 • Da waɗannan kuɗaɗen da aka bayyana, Amurka tana samar da kusan dala biliyan 3 na tallafi ga al’umma da bala’i ya shafa don kai ɗauki ga waɗannan al’ummomin daga yankin Tabkin Chadi, Sudan ta Kudu, Somaliya, da Habasha tun farkon kasafin kuɗin shekarar 2017.
 • Daga cikin sabbin kuɗaɗen da aka bayyana, kusan dala miliyan 184 ne aka keɓe don al’ummomi daga Sudan ta Kudu waɗanda bala’i ya shafa, fiye da dala miliyan 110 domin al’ummomi daga Habasha waɗanda bala’I ya shafa, fiye da dala miliyan 110 domin al’ummomi daga Somaliya waɗanda bala’i ya shafa, kuma fiye da dala miliyan 128 don al’ummomi daga Nijeriya da kuma ƙasashen yankin Tabkin Chadi waɗanda bala’I ya shafa.
 • Wannan ya kawo jimmillar tun farkon kasafin kuɗin shekarar 2017 ga kusa da dala biliyan 1.2 don al’ummomi daga Sudan ta Kudu waɗanda bala’i ya shafa, kusan dala miliyan 565 don al’ummomi daga Habasha waɗanda bala’i ya shafa, fiye da dala miliyan 602 don al’ummomi daga Somaliya waɗanda bala’i ya shafa, da kuma fiye da dala miliyan 655 domin al’ummomin ƙasashen yankin Tabkin Chadi waɗanda bala’i ya shafa

Tambaya: Yaya yanayin ba da agaji ga al’ummomin da bala’i ya shafa yake a cikin waɗannan ƙasashen Afrika?

 • A yankin Tabkin Chadi da Sudan ta Kudu, shekaru da dama na rikici sun haddasa matsanancin ƙarancin abici. A Somaliya, tashin hankalin da ke ci gaba ya daɗa wahalar da mutane ke ji daga matsananci fari na tsawon lokaci. A Habasha, fari mai ci gaba ya ƙara tsananin yanayin wadatar abinci wadda a da ma a taɓarɓare take.
 • Saurin kwararowar taimako daga Amurka, tare da na wasu masu ba da tallafi dabam, ya tsayar da yunwar game-gari da taimakawa wajen inganta yanayin rayuwar mutane a cikin dukkan waɗannan ƙasashen. Amma duk da hakan matsanciyar yunwa da cutar da ke haɗe da ita naci gaba da zama barazana ga miliyoyin rayukka.
 • Duk da yake wannan ba da tallafi ga waɗanda suke fuskantar bala’i ya kasance muhimmin abin ceton rai ne, wannan tallafi ba zai magance waɗannan masifofi ba, waɗanda mafi yawancinsu mutun ne kan haddasa su, don haka hana faruwarsu na yiwuwa.
 • Amurka tana kira ga duk ɓangarorin da ke cikin waɗannan rikice-rikicen da su daina faɗace-faɗace su kuma ba masu aikin agaji damar isa wurin al’ummar da ke bukatar taimako cikin kwanciyar hankali kuma ba tare da an yi musu katsalandan ba.
 • Muna kuma kira ga sauran masu ba da tallafi da su ƙara kashin kuɗaɗen tallafinsu don cimma biyan bukatar waɗannan bukatu taimakon waɗanda bala’i ya shafa.

Tambaya:  Yaya Amurka take yi game da rahotonni na kwanan nan na cewa al-Shabaab tana moriya da ƙaruwar agaji ta kuɗi da cakin kuɗi a Somaliya da kuma rahotonnin cewa an kama kayayyakin Amurka a lokacin samamen da hukomomin Somaliya suka yi?

 • A saninmu al-Shabaab ba ta karkatar da kayan agajin Amurka ba.  Za mu yi binciken ƙaƙaf a kan shaidar akasin hakan, domin ɗaukar mataki kamar yadda ya dace.
 • Muna kan taimakon hukumomin Somaliya da kuma Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) a yayinda suke binciken yiwuwar karkartar da agajin abinci.
 • Za mu ɗauki matakai da sun dace na magance abun nan da nan tare da WFP da kuma gwamnatin Somaliyar, don karɓo duk wani agajin da an karkatar da shi, da kuma yin aiki ta ganin an daƙile karkatawar a gaba.

Tambaya: Wace garkuwa Amurka take da a shirye don lura da shirye-shirye da kauce wa karkatawa da agaji Amurka?

 • Muna ba da muhimmanci ga duk wani zargin cewa an yi amfani da tallafinmu ga waɗanda bala’i ya shafa ta wata hanya wadda ba ta dace ba, kuma ko kaɗan ba ma ƙyale zamba, ɓanna, da gwagwarmaya da dukiyar amurkawa masu biya haraji.
 • Mun yi aiki kuma muna ci gaba da aiki tare da abokan hulɗarmu don tabbatar da sun tanadi hanyoyin masu ƙarfi na sauƙaƙa faruwar mugun abu. Tallafin Amurka ga waɗanda bala’i ya shafa domin yara ne, da mata da kuma maza da suke ciki bukata, kuma muna ba da fifiko ga tabbatar da an yi amfani da dukiyar masu biyan haraji cikin hikima, da kyau kuma daidai da makasudin da aka tsara su bisa gare shi.
 • A lokutta da yawa mun yi aiki da masu kula dabam waɗanda suke zaman kansu kuma da suke da cikakkar fahimtar al’adu da kuma ainihin yanayin da ake ciki a yakin, don tabbatar da ingancin ayyukan tsare-tsaren. Wannan ƙarin kulawar yana taimakawar musamman a mawuyacin yanayin inda muke aiki.
 • Muna yi binciken ƙaƙaf a kan shaidar ko zargin cewa an yi amfani da kuɗaɗen Amurka ta hanyar da ba ta dace ba, kuma mu ɗauki mataki kamar yadda ya dace.

Tambaya: Mu ji rahotonnin cewa akwai yiwuwar yunwa ta sake dawowa a Sudan ta Kudu. Minene Amurka take yi domin hana hakan?

 • Matsalar da yanzu ake fuskanta a Sudan ta Kudu, har ma da ƙaruwar yiwuwar yunwa, abu ne da mutane suka haddasa daga ɓangarorin da ke cikin rikicin. Ko da yake Hukumar Abinci da Noma ta MDD ta ruwaito da kasancewar madaidaicin yawan ruwa sama a Sudan ta Kudu ga damunar yanzu, yawan kayan gona ya ragu sosai saboda rikicin da ke ci gaba. Amurka tana kira ga waɗannan mafaɗatan da su mayar da gurinsu na siyasa a gefe, su koma ga zancen sulhu da yankin yake ɗaukar nauyinsa su kuma gaggauta ba jin daɗin al’ummominsu fifiko.
 • A bisa ga sabon bayanin ‘Integrated Food Security Phase Classification’- wani rahoto kan wadatar da abinci daga gwamnatin Sudan ta Kudu, MDD, da kuma wasu abokan hulɗa masu ba da tallafii – mutane miliyan 5.3 – kusan kasha 50 bisa ɗari na al’ummar yanzu – suka bukaci agajin abinci a watan janairu, wani ƙari na 40 bisa ɗari ke nan bisa ga yadda ya kasance a daidai wannan lokaci sherakar da ta gabata. Idan an sami ɗaukewar agaji na tsawon lokaci, yunwa za ta yiwu a wasu sassan Sudan ta Kudu a cikin ‘yan watanni masu zuwa, musamman ma a yakuna inda al’umma sun rigyaya suna fuskantar matsanancin ƙarancin abinci.
 • Amurka ita kaɗai ta kasance mai ba da tallafi ga Sudan ta Kudu mafi girma ta wurin ba da kusan dala biliyan 3.1 tun farkon rikicin a disambar 2013, ciki har da wannan kuɗaɗen na bayan nan.
 • Tallafin Amurka yana samar wa kimanin mutun miliyan 1.4 da abinci na ceton rayukka a kowane wata. Tun farkon rikicin a 2013, USAID ta samar wa Sudan ta Kudu kimanin tan 680,000 na agajin abinci na gaggawa – wanda ya isa ya ciyar da mutane miliya 3.7, ko kuma kusan yawan mutanen Jihar Connecticut, a tsawon shekara ɗaya.
 • A shirin zuwan lokacin rani – lokacin shekara da yunwa ta fi tsanani – wanda ya fara a Janairu, watanni uku kafin lokaci da aka saba gani, USAID na ci gaba da taimakawa wajen shirya wuraren ajiye abincin agaji a yankuna da suka kasance sun shafi yadda aka yin amfani da su a ƙasar don taimaka wa iyalai marasa ƙarfi. Ƙari ga hakan, USAID na samar da muhimmin agajin abincin gina jiki, kiwon lafiya na gaggawa, da ingantaccen ruwan sha, bayan gida da ƙunshin kayan tsabtar jiki, domin kiyaye mutane daga mutuwa da yunwa, tare da hana yaɗuwar cuta kamar su cutar gudawa, wacce kan iya zama babban sanadin mutuwa a lokacin matsalar abinci.
 • Ma’aikatar Harkokin Waje ita ma tana ba da goyon baya ga ‘yan gudun hijira Sudan ta Kudu fiye da miliyan 2.4 waɗanda suka gudu zuwa ƙasashe maƙwabta na yakin.  Wannan agaji ya haɗa da tsaro mai muhimmin tasiri da agaji ga ‘yan gudun hijirar da bala’i ya shafa a Afrika ta Tsakiya, Jamhuriyar Kongo, Habasha, Sudan da Uganda, waɗanda dukkansu suna fama da ƙoƙarin cimma biya buƙatun al’ummominsu.
 • Masu fafutukar ba da tallafi ga waɗanda bala’i ya shafa suna aiki ba ƙyauƙyautawa kuma cikin kasada don isar da muhimmin agaji ga mutanen da suke cikin bukata a ko’ina cikin ƙasar. Ya zama wajibi ga dukkan ɓangarorin da ke cikin rikicin da su daina hana ƙoƙarin kai agaji su kuma bar abinci da sauran muhimmin taimako su isa ga mutanen da sun fi bukatar su.
 • Amurka tana duƙƙufa wajen ƙoƙarin kawo ƙarshen tashin hankalin game-gari, tokarar tushin matsalar faɗace-faɗace tsakanin ‘yan ƙasa, taimaka wajen shaho kan munannan matsalolin da ke shafar mutane, da ƙarfafa yin adalci dangane da kurakurai da cin zarafin ɗan Adam da aka yi lokacin rikicin.

Tambaya: Ko wani kashi daga cikin wannan sabon tallafi zai je ga Oxfam?

A’a. Babu kaso ko ɗaya daga cikin wannan sabon tallafin da zai je ga Oxfam.

Tambaya: Yaya za ku tabbatar da ba za a yi amfani da ko ɗaya daga cikin waɗannan kuɗaɗen ba don ci da gumin wasu ta hanyar jima’i?

 • Amurka ja-gaba ce wajen ba da tallafi ga waɗanda bala’i ya shafa a faɗin duniya kuma muna ba da muhimmanci ga nauyin da ya rataya a wuyanmu na tabbatar da cewa ma’aikata da abokan hulɗa suna aiki tuƙuru wajen kare al’ummomin da suke wa aiki daga cin zarafi ta hanyar jima’i ko yin wulaƙanci.
 • Gwamnatin Amurka ko kaɗan ba ta ƙyale cin zarafi ta hanyar jima’i da wulaƙanci.
 • Lokacin da aka jawo hankalinmu a kan wani zargin cin zarafi ta hanyar jima’i ko yin wulaƙanci, mukan buƙaci ƙungiyar da ta ɗauki matakai da ya kamata a ɗauka don duba al’amarin.
 • Muna zato abokan hulɗarmu sun tsara hanyoyin kai koke-koke da kuma na bincike tare da ƙaƙƙarfan manufofi da ke ba wasu damar kawo rahoto. Rashin tsare-tsare na hana ko ɗaukar mataki a kan cin zarafi ta hanyar jima’i ko wulaƙanci na iya zama dalilin tsayar da ba da kuɗaɗen tallafi game da ƙungiyoyi.

Sakonnin Email
Domin samun sakonnin mu ko kuma ganin zabin da ka yi a matsayin mabiyin mu, shigar da bayanan ka a kasa